Wani Babban Dan Kungiyar Boko Haram Tare Da Wasu Yan Kungiyar Uku Sun Mika Wuya Ga Sojoji 

Wani babban jigo a kungiyar Boko Haram, Konto Fanami da kuma wasu yan ta’adda guda uku sun mika wuya ga rundunar sojin Najeriya a ranar Litinin.

Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Sani Usman shine ya bayyana haka a Abuja.

Usman yace yan ta’addar hudu da suka tuba, da kansu suka bar maboyarsu suka kuma mika kansu ga bataliya ta 120 dake Goniri.

Ya bayyana Fanami a matsayin “Amir na maboyar yan ta’addar Boko Haram dake, Kafa da suke gudanar da ta’addanci a yankin Ajigin-Talala-Mungusum.”

“Lokacin da ake musu tambayoyi sun tabbatar da cewa sun bar ta’addanci saboda irin yawan wahalhalun da suke fuskanta da kuma fahimta da sukayi cewa shugabaninsu sun batar dasu daga kan hanyar gaskiya.

” Sun kuma kara fadin cewa cikin kuskure an juyar  musu da tunani akan musulunci,Sojin Najeriya da kuma Jama’a baki daya.
“Tubabbun yan ta’addar da suka tuba sunyi danasanin shigarsu aiyukan ta’addanci sun kuma yaba da yadda hukumomin soji suka karbesu da kuma basu  kulawa lokacin da suka mika wuya,”kakakin sojin yace.

Yayi kira ga sauran ragowar yan kungiyar ta Boko Haram kan su mika wuya.

Usman yace anyi cikakken tsari domin karbar duk wani dan kungiyar da ya yarda ya mika wuya ya bar aikata ta’addanci ya kuma tabbatar musu da cewa za a kula dasu cikin mutunci

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s