Shin ‘yan Nigeria sun fara gajiya da APC ne?

Guguwar canji ta APC da Buhari ya jagoranta ta kada jam’iyyar PDP a zaben 2015

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kafa tarihi a shekarar 2015 a matsayin jam’iyyar da dan takararta ya doke shugaba mai ci a kasar.

Kazalika APC ta lashe mafi yawa daga cikin zabukan ‘yan majalisar tarayya da na jihohi da kuma na gwamnoni.

Sakamakon zaben ya sa jam’iyyar ce take mulki a dukkan jihohin arewacin kasar idan ban da jihar Gombe da kuma Taraba.

A kudu maso yammacin kasar ma, jam’iyyar ce take mulki a jihohi hudu cikin shida.

Lamarin ya dada kyautatuwa ga jam’iyyar bayan an gudanar da zabukan gwamnoni a jihohin Kogi da Ondo inda jam’iyyar APC ta sake samun nasara.

Wannan ya sa jihohi kadan ne jam’iyyar ta rasa a yankin arewacin Najeriya da yankin kudu maso yammacin kasar.

Sai dai kuma, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta doke APC a zaben cike-gurbi na mazabar jihar Osun ta yamma a majalisar dattawan kasar bayan rasuwar Sanata Isiaka Adeleke, tsohon gwamnan jihar.

Marigayi Adeleke dai ya wakilci mazabarsa ta Osun ta yamma ne karkashin jam’iyyar APC saboda haka sai kaninsa, Ademola Adeleke, ya nemi ya gaje shi a matsayin wakilin mazabar Osun ta yamma a majalisar dattawan Najeriya a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamnatin jihar Osun da kuma reshen jihar Osun na jam’iyyar APC ba su so ya maye gurbin yayan nasa ba.

Sun fi so Mudasir Hussein ya wakilci mazabar. Wannan ne ma ya sa a lokacin yakin neman zaben suka yi ta cewa “kujerar sanatan ba ta gado ba ce.”

Saboda haka, Ademola Adeleke ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP bayan ya ga ba zai samu tikitin jam’iyyar APC mai mulki ba.

Bangaren Ali Modu Sherrif na PDP ne ya ba shi tutar jam’iyyar PDP.

Bayan ya zama dan takarar jam’iyyar PDP mai hamayya ya samu gagarumar nasara kan dan takarar APC Mudasir Hussein.

Ademola ya samu kuri’u 97,480 bayan ya yi nasara a kananan hukumomi tara cikin 10, yayin da Mudasir ya sami kuri’u 66,116 bayan ya lashe zabe a karamar hukuma daya cikin 10.

Da take tsokaci kan sakamakon zaben, jam’iyyar APC ta bayyana abin da ya sa ta ba Mudasir Hussein tikitin jam’iyyar, maimakon Ademola Adeleke.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, reshen jam’iyyar jihar a Osun ya ce jam’iyyar ce ta hana Mudasir, wanda da yake wakiltar Osun ta yamma a majalisar dattawan Najeriya, takarar Sanata a shekarar 2015 domin marigayi Sanata Isiaka Adeleke ya samu ya zama mazabar Osun ta yamma a majalisar dattawa a lokacin.

Sakon ya kara da cewa wannan ne ya sa jam’iyyar ta ga ya dace ta ba wa Mudasiru damar komawa kujerar bayan rasuwar Adeleke.

Shi kuwa gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola cewa ya yi ya koyi darasi daga sakamakon zaben, kuma jam’iyyarsa za ta dawo da karfinta.

Dan takaran jam’iyyar adawa ta PDP, Ademola Adelke, ya ka da dan takaran jam’iyyar APC mai mulki a zaben cike gurbin wakilin Osun ta yamma a majalisar dattawan Najeriya

A ganin bangaren Ahmed Makarfi na PDP, nasarar babbar jam’iyyar adawar a kan APC mai mulki na nuna cewa “‘yan Najeriya sun juya wa APC baya.”

A sanarwar da ta fitar bayan an bayyana sakamakon zaben, bangaren Makarfi na jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ‘yan Najeriyar sun juya wa jam’iyya mai mulkin baya ne domin sun gane abin da ta kira “yaudarar APC.”

Sai dai kuma wasu masana harkokin siyasa na ganin ba lallai ba ne kayen da jam’iiyar APC ta sha a zaben cike-gurbin ya zama wata manuniya ce kan yadda ‘yan Najeriya suka fara juya wa jam’iyyar baya ba.

Farfesa Jibrin Ibrahim, masani ne kan siyasa a Najeriya kuma ya shaida min cewa mai yiwuwa ne tausayin rasuwar Isiaka Adeleke ya kasance daya daga cikin dalilan da suka sa aka zabi kaninsa.

Ya kara da cewa irin farin jinin ‘yan takarar na iya kasancewa daya daga cikin dalilan da suka yi tasiri kan sakamakon zaben.

Ga abin da Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce game zaben, sai ku latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraro.

Ko wane zabe dan takaran ake dubawa’

Ko dai ‘yan Najeriya sun juya wa APC baya ko kuma a’a, za a iya gane hakan ne a babban zaben shekarar 2019.

 

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s