Mun shirya tsaf don kwace mulki daga APC – PDP

PDP ta ce ‘yan Najeriya sun sha wuya a hannun APC

Babban jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, ta ce ta shirya tsaf domin kwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulkin kasar a 2019.

Manyan jami’an PDP sun bayyana haka ne a wurin taron da suka gudanar a Abuja ranar Talata.

Akasarin jiga-jigan jam’iyyar ta PDP da suka tattauna da BBC a wurin taron, sun ce jam’iyyar ta yi nadamar kura-kuran da ta tafka a baya amma a shirye take ta gyara su domin sake mulkar Najeriya.

Hakan ne ma ya sa, a cewar daya daga cikinsu Sanata Ahmad Ningi, jam’iyyar ta kafa kwamitoci biyu domin tsawatarwa da kuma daidaita ‘yan jam’iyyar.

“Mun yi damarar da za mu iya yin fito-na-fito da kowacce jam’iiya. Za mu kwace mulki daga APC a 2019”, in ji Sanata Ningi.

Ya kara da cewa, “Za mu sake yin taron koli na jam’iyya domin karawa shugabannin riko wa’adi domin su shirya yadda za a gudanar da babban taro. Ba ma so mu sake yin kura-kuran da za su sa wani ya kai mu kotu. Shi ya sa muka kafa kwamitin tsawatarwa saboda a baya ‘yan jam’iyyarmu ba su da da’a, kowa yana yin abin da yake so. Don haka ba za mu bari kowa ya taba jam’iyyar ba”.

Sanata Ningi ya ce ‘yan Najeriya sun dandana kudarsu a hannun ‘yan jam’iyyar APC don haka ba za su sake yin kuskuren zabar jam’iyyar ba.

Wannan ne dai karon farko da shugabannin jam’iyyar ke gudanar da taro tun bayan hukuncin da kotun kolin kasar ta zartar daya bayyana Sanata Ahmed Makarfi a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s