Daga Zauren Fiqhu: Hanyoyin Shiga Aljanna Masu Sauki

 

BIN ALLAH DA RIKON ZUMUNCI

Hadisi daga Sayyiduna Abu Ayyub Al Ansariy (ra) yace :

“Wani Mutum yazo wajen Manzon Allah (saww) sai yace “Ka nuna min wani aiki wanda idan nayishi zai kusantar dani zuwa Aljannah kuma ya nisantar dani daga wuta”.

Sai yace masa : “KA BAUTA MA ALLAH KADA KA HADASHI DA KOMAI. KA TSAI DA SALLAH, KA BAYAR DA ZAKKAH, KUMA KA SADAR DA MA’ABOCIN ZIMUNCINKA”.

Yayin da mutumin ya juya baya, Sai Annabi (saww) yace : “Idan yayi riko da abinda aka Umurceshi, lallai zai shiga Aljannah”.

Aduba Sahihu Muslim juzu’i na 1, shafi na 43.

BAYANI

********

_Wadannan ayyukan da aka lissafa acikin hadisin nan, ayyuka ne masu sauki ga duk wanda Allah ya saukaka masa. Amma suna da mutukar wahala ga mafiya yawan Mutane.
Ga misali :
1. TSARKAKE BAUTA GA ALLAH : Da yawan mutane (Har ma wasu Maluman) yanzu riya da son duniya da neman girma ya mamaye zuciyarsu. Tun daga Wa’azi ko Muhadharah zaka ga mutum Qarara yana son nuna cewa shi wane ne.

2. SALLAH : Itama riya tayi katutu azukatan mutane game da ita. Kaga mutum yana sallah kamar wanda cinnaka ke cizonsa (Idan shi ka’dai ne).

Amma idan agaban Jama’a ne sai kaga yafi yinta cikin nutsuwa!.
Kaga mutum yana sallah yana karairaya duk wai son ache “Ya iya”. Mutane sun mance cewar ikhlasi Allah yake bukata daga bayinsa ba wai yawan ba.

3. ZAKKAH : Ita ma kamar dai sallar ne. Masu kudin basu cika son fitarwa ba. Idan ma sun fitar da zakkar tasu, atsakaninsi suke rarrabewa.

Kai ka fitar ka kawo ma iyalaina, nima na fitar na kaima iyalanka.. Ita ce siffar zakkar masu kudin zamani.
Wani kuma idan ya tashi fitarwa haka zai rarraba Naira dari biyu ko dari biyar biyar.. Maimakon ya dunkule ya bayar.

4. ZUMUNCI : Shima yanzu mutane sunyi watsi dashi. Kaga ‘yan uwan juna ana zaune agida daya ko unguwa guda amma babu ruwan wani da wani.

Wannan ba daidai bane. Duk mai son samun rahamar Allah lallai ne ya rike zumuncinsa ya rungumi ‘yan uwansa koda su sun watsar dashi.
Allah yasa mu dace, Aameen.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s