Akan yaron aka fara yin dashen hannu a duniya

Zion yace a okacin da ya ke shekaru biyu a duniya, dole aka yanke masa hannaye saboda ba shi da lafiya

Yaro na farko da aka fara kafa tarihi a duniya, da kuma aka yi wa dashen hannu ya fara yin wasan kwallon gora da hannun kamar yadda likitansa ya bayyana.

Shekaru biyu kenan da aka yi wa Zon Harvey aikin da aka dasa masa hannun, likitocin da ke kula da yaron sun ce sun mamakin yadda lokaci kalilan hannun ya saje da jikinsa.

Zion mai shekara 10, ya samu ci gaban ne bayan dashen hannun da kwararrun likitoci suka yi masa, a halin da ake ciki yana iya cin abinci, har ma da yin rubutu.

Likitocin sun ce duk da cewa hannun da aka dasa masa wani ne ya ba shi kyautarsa, amma kwakwalwarsa ta karbi sabon bakon al’amarin da ya zo mata katsahan.

Daya daga cikin likitocin da suka yi wa Zion aiki a asibitin yara na Philadelphia wato Dakta Sandara Amaral, ta shaidawa BBC cewa a kodayaushe ana samun ci gaba kan yadda yaron ke amfani da hannun tamkar tun ainahi na shi ne.

Ta kara da cewa abin mamakin shi ne yadda Zion ke rubuta sunan shi da wasu kalmomi cikin sauri, ya kuma kamo fuskar mahaifiyarsa da hannun tare da sumbatar kumatunta ba kamar farkon aikin da baya ma iya motsa hannun ba.

Kungiyar likitocin da suka yi wa Zion aiki, sun wallafa dukkan bayanan yadda aka yi wa yaron aiki tun daga farko har karshe, da ci gaban da aka samu a wata mujallar Lancent, a shafin da ke bayani a kan yara wato Child and Adolescesnt Health jounal.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s