Wadanda Suka fice Daga Jam’iyar  PDP Zasu Dawo – Jonathan 

Tsohon shugaban kasa Gudluck Jonathan yace jam’iyar tamkar mayen karfe ce da zata jawo duk wani danta da ya sauya sheka zuwa wata jam’iyar.

Jonathan ya fadi haka ne a wurin wani taron jiga-jigan jam’iyar da akayi a daren jiya a hedikawatar jam’iyar dake Wadata Plaza.

Tsohon shugaban kasar yace a zahiri take cewa yan Najeriya, har yanzu sun yarda da tasirin jam’iyar adawa.

Wannan a zahirance yake idan akayi duba da irin martani da suke mayarwa bayan hukuncin da kotun koli ta yanke kan rikicin shugabancin jam’iyar.

Jonathan ya shawarci dukkanin yayan jam’iyar da kuma magoya bayan jam’iyar da su mai da hankalinsu wajen gina jam’iyar.

” Har yanzu yan Najeriya sun yarda da PDP saboda lokacin da kotun koli ta yanke hukunci nayi mamaki matuka wasu mutane sun kirani wasu kuma sun turo min sako, ” yace.

“Su bama yan siyasa bane,  amma murna suke PDP ta fita daga matsala saboda sun damu cewa jam’iyar PDP zata mutu.

” Idan kuwa wadanda ba yan PDP ba za suyi murna da nasarar PDP duk da farfaganda da ake yadawa akan jam’iyar  kenan mutane har yanzu sun yarda da PDP.

“PDP jam’iya ce da yan Najeriya har yanzu  suka yarda da ita. ”

Ya kuma roki yan jam’iyar da su sake ginata, inda yayi musu tabbacin cewa mutane da dama da suka bar jam’iyar saboda rikicin shugabancin jam’iyar zasu dawo.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s