Rundunar sojin Najeriya kara tace ta gano wata maboyar yan kungiyar Boko Haram dake yankin tafkin Caji.
A wata sanarwa, Timothy Antigha mai magana da yawun rundunar ta 8 dake Borno, ya jiwo daga bakin Stevenson Olabanji babban kwana rundunar yana bayyana haka lokacin da yakaiwa sojojin bataliya ta 118 dake karkashin rundunar.
Sanarwar tace babban Kwamandan yayi kalaman karfafa gwiwar sojojin inda ya umarce su da suka sance cikin shiri a koda yaushe.
Sanarwar ta rawaito Olabanji yana fadawa sojojin cewa a koda yaushe za a iya bada umarnin kai hari akan maboyar yan Boko Haram, harin ka iya zamowa na karshe da zai kawo karshen hare-haren da Boko Haram ke kaiwa.
Antigha yakara da cewa karshen rikicin Boko Haram na gab da faruwa.