Labarai A Takaice: Buhari Ya Matsu Ya Dawo Najeriya………

Ministar kula da bunkasa masan’antu, zuba hannun jari da kuma cinikayya ta Najeriya, Aisha Abubakar, ta ce a shekara ta 2015 da ta gabata kadai, akalla naira triliyan 7 aka kashe domin shigo da kayan masaufi, da sauran kayayyakin da aka sarrafa a kasashen ketare zuwa cikin kasar.

– Rahotanni daga garin Calabar da ke jihar Cross Riners a kudancin Najeriya, na cewa sama da mutane 20 sun kwanta dama sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan mai na Linc Oil da ke unguwar NPA esukutan.

– A Nijeriya, an tattauna da matasan Igbo daga kungiyar Ohaneze Ndigbo, da kuma gamayyar kungiyoyin matasan arewa.

– Rahotanni daga Afirka ta Kudu sun ce an yi wa shugaban kasar Jocob Zuma tayin afuwa da za a bashi dala miliyan dari da hamsin, saboda ya sauka daga kan mulki.

– Dubban ‘yan kasar Turkiya ne suka yi fita zuwa titunan kasar domin bukukuwan zagayowar ranar da aka yi yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba, wanda yayi sanadin hallaka mutane 260 yayinda wasu 2, 196 suka jikkata.

– Rahotanni daga kasar Senegal sun ce mutum 8 ne suka mutu a wani turmutusu da ya faru, sakamakon wata arangama tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa biyu.

– Garbine Muguruza mai wakiltar kasar Spain ta samu nasarar lashe kofin gasar kwallon Tennis na Wimbledon, karo na farko, bayanda ta samu nasara kan Venus Williams a wasan karshen da ya gudana a yau a Birtaniya.
– Shugaba Buhari ya matsu ya dawo gida Najeriya domin karyata Rahotannin cewa yanayin lafiyar sa bazai bari ya ci gaba da mulki ba.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s