Illar Shaye-Shaye: Wani Matashi Ya Cakawa Kansa Wuka

 

Wani Matashi mai suna Umar Mande, mai kimanin shekaru 35, ya cakawa kansa wuka a garin Potiskum ta jihar Yobe. Amma cikin ikon Allah bai mutu ba. 

Yadda al’amarin ya faru kuwa shine, shi dai wannan matashi, shi da abokanansa suna shaye shayen su a wata Mashaya da ake kira Dorawa a cikin garin Potiskum, sai rikici ya hada su akan Giyar Wiski, wadda takai ga har shi Umar Mande ransa ya baci, saboda ba a bashi ya sha ba.

To wannan bacin ran ne yasa ya cakawa kansa wuka a cikin sa, inda nan take ya fadi, aka dauko shi cikin gaggawa zuwa babban Asibitin Potiskum. Yanzu haka dai Likitoci suna kokarin ceto rayuwarsa a babban Asibitin Potiskum, sannan kuma Jami’an tsaron ‘yan Sanda, suna binciken lamarin.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s