Kasar Amurika Ta Fara Yinkurin Kwace Wasu Kadarori Daga Hannun Diezani  Da Wasu Mutane

Gwamnatin Kasar Amurika  ta shigar da kara domin kwace kadarori da darajarsu takai dala miliyan $144 wanda aka samu daga badakala a harkar ma’aikatar man fetur ta Najeriya.

Bangaren shari’ar kasar Amurika domin kwato dukiyar da aka samu ta haramtacciyar hanya.

Wasu yan kasuwa biyu Kola Aluko da Jide Omokore sune suka bawa tsohuwar ministan mai ta Najeriya Diezani Alison-Madueke cin hancinc kudade tsakanin shekarun 2011- 2015  domin a basu kwangila.

An rawaito cewa Diezani tayi amfani da matsayinta wajen nemowa kamfanonin  bogi  na Aluko da Omokore  kwangilar mai a kamfanin mai na kasa NNPC.

Duk da kamfanonin sun gaza ka’idojin kwangilar rahotanni sun nuna cewa an basu damar su sai da danyen man fetur na Najeriya da darajarsa takai dala biliyan $1.5.

Aluko da Omokore sun siyawa Diezani kadarori miliyoyin daloli a  biranen London da Amurika, tare da siyar kayayyakin kawatan gidajen na miliyoyin dala.

Karar ta bukaci kwace jirgin ruwan Omokore mai suna Galactica da darajarsa takai dala miliyan $80 da kuma wani gida a birnin New York da darajarsa takai dala miliyan $50.

Cikin takardun karar harda wata murya da aka nada inda a ciki Diezani ke gargadin mutanen biyu kan su rage kashe mata kudi don gudun kada hankalin mutane yakai kan alakarsu.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s