Jam’iyar APC Ta Dakatar Da Mai Taimakawa Shugaban Kasa Da Wasu Mutane 19

Shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam’iyar APC reshen jihar Enugu sun amince da gagarumin rinjaye da a dakatar da wasu yan jam’iyar su 20 bayan da aka same su da rashin da’a da kuma yiwa jam’iya zagon kasa. 

Cikin wadanda aka dakatar akwai mataimakin shugaban jam’iyar na Jiha, Adolphus Ude, shugabar mata Queen Nwanko, da kuma mai taimakawa Shugaban a bangaren ha kawo sauyi a harkar Shari’a, Juliet Ibekaku.

Joe Orji shine yayiwa manema labarai jawabi, inda yace yan jam’iyar sunyi allawadai da mamaye ofishin jam’iyar da Ude da mukarrabansa sukayi a ranar Litinin 3 Ga watan Yuli.

Mista Orji wanda shine shugaban kwamitin sasanta rikicin jam’iyar a jihar ya kuma ce Ben Nwoye, shine  halattaccen shugaban jam’iyar.

Yace masu ruwa da tsakin sun amince da dakatar da  mataimakin shugaban jam’iyar da kuma mutane 19 dake da hannu a mamaye ofishin jam’iyar a ranar 3 ga watan Yuli.

Da yake karin haske kan zaman da masu ruwa da tsakin sukayi, Orji yace jam’iyar baza ta amince da rashin da’a ba.

Yace jam’iyar APC tayi alkawarin kawo sauyi saboda haka dole sauyin yafara daga cikin jam’iyar.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s