Daga Zauren Fiqhu: Sunan Allah Mafi Girma

Wani mutum yana addu’a bayan ya idar da Sallah agaban Manzon Allah (saww), sai yace:
“ALLAHUMMA INNEE AS’ALUKA BI ANNA LAKAL HAMDU. LA ILAHA ILLA ANTA BADEE’US SAMAWATI WAL ARDHI.

YA DHAL JALALI WAL IKRAAMI.. YA HAYYU YA QAYYUM”.

Sai Manzon Allah (saww) yace “HAKIKA WANNAN MUTUMIN YA ROKI ALLAH DA SUNANSA MAFI GIRMA. WANDA IDAN AN KIRASHI DASHI YAKE AMSAWA, KUMA IDAN AN ROKESHI DASHI YANA BAYARWA”.

♦ Sahihin hadisi ne. Aduba:
SUNANUT TIRMIZY hadisi na 3,544.
SUNANU IBNI MAAJAH hadisi na 3,858.
MUSTADRAK NA HAKIM, hadisi na 1,856.

Malamai suka ce duk wanda yake neman biyan bukatarsa da gaggawa, Idan ya idar da Sallar farillah, ko nafila da rana ko da daddare, yayi ma Shugabanmu (saww) salati gwargwadon iko sannan ya karanta wannan addu’ar (ISMULLAHIL A’AZAM) ya fadi bukatarsa da larabci ko da wani yaren da zai iya. sannan ya Qara yin wasu salatai abisa Shugaba (saww).

Insha Allahu duk wanda yayi wadannan abubuwan kamar yadda aka fada dinnan zai ga abun mamaki wajen samun biyan bukatarsa cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s