Wani Manomi Ya Kirkiri Fasahar Yin Wurin Ajiye Albasa A Cikin Gona 

Wani manomi dake zaune a jihar ya kirkiri yadda za a ajiye albasa har tsawon watanni shida batare da ta lalace ba.

Da yake magana da jaridar Daily Trust a garin Kaduna, manomin albasar, Abubakar Jibril Madigawa, ya bayyana cewa lokacin da ya zama ba a samun riba a noman tumatur bayan da aka samu annobar tsutsa da ta shafi gonaki da dama, sai ya yanke shawarar komawa noman albasa amma kuma ya fuskanci matsalar wurin ajiya.

” Domin maganin matsalar, na kirkiri fasahar a ajiye albasa a cikin gona, da za a iya ajiye albasar har tsawon watanni shida ba tare da ta lalace ba.

” Ina sai da albasar lokacin da naga farashinta yayi dai-dai da yadda nake so,saboda sabon tsarin ajiyar ya nasa albasar ta dade sosai,” manomin yace.

Yace tsarin yana rage asara da kaso 70 zuwa 80 inda yace hakan yana bashi damar samun riba sosai.

Madigawa yayi nuni da cewa, tun farko sai da yafara samar da gurin ajiyar na gwaji a gidansa, inda ya gwada kuma ya amince da ingancinsa kafin daga bisani ya samar da babba a gonarsa.

Ya bayyana sabuwar fasahar a matsayin wata hanya da manoma zasu rage asara.

Madigawa ya shawarci gwamnati da ta taimakawa manoma da bashi domin su samu su gina irin wurin ajiyar

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s