Har Yanzu Ina Cikin Dimuwa Da Kaduwa – Modu Sharif   

Korarren shugaban jam’iyar PDP, Sanata Ali Modu Sharif ya tattara yanasa yafice daga Wadata Plaza Hedikawatar jam’iyar bayan da yasha kayi a shari’ar da ake kan rikicin shugabancin jam’iyar.

Sharif yace har yanzu yana cikin dimuwa sa da kuma  kaduwa da hukuncin kotun da yarabashi da mukaminsa na shugabancin jam’iyar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun bangarensa, Bernard Mikko, yafitar  Sheriff yace  har yanzu yana jiran bayani daga kan hukuncin na kotun daga bakin lauyoyinsa.

” Mun karbi hukuncin kotun kolin kan shugabancin jam’iyar PDP  cikin kaduwa. Duk da cewa muna jiran cikakken hukuncin kotun a rubuce daga hannun lauyoyin mu inda zasu yimana cikakken bayanin hukuncin,  a mataki na wucin gadi muna kira ga mutane da su kasance masu yiwa Najeriya addu’a.

” Amma kuma zamu cigaba da kiran da muka saba yi a fili  cewa jam’iyar mu dole a mayar da ita wajen mutanen da suke a kasa domin ganin cewa sun zabi shugabannin jam’iyar da kansu da kuma wadanda zasu wakilce su a zabukan ko wane mataki. dole a girka dimokwaradiyar cikin gida a cikin jam’iyar,” sanarwar tace.

Wata motar yan sanda ce ta kwashe kayan sheriff daga hedikawatar jam’iyar.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s