Yan sanda Sun Kama Wani Mutum Da Ya Shirya Yin Garkuwa Da Kansa Domin Ya Karbi Miliyan 60 A Wurin Yayansa

Yan sanda a jihar Lagos, sun kama wani mutum a ranar Alhamis, da yayi kokarin karbar miliyan 60 a hannun dan uwansa bayan da yayi karyar anyi garkuwa dashi. 

Kakakin rundunar yan sandan jihar Lagos,ASP Olarinde Famous-Cole ya tabbatarwa da manema labarai kama mai laifin.

A cewar Famous-Cole, ranar 3 Ga. Yuli, wani mutum Victor Udo yakaiwa rundunar rahoton cewa wasu mutane da ba’asan ko suwaye ba sunyi  garkuwa da kaninsa mai suna Ufom Edet  Udoh, a yankin Liverpool dake Apapa a Jihar ta Lagos.

Famous-Cole yace jami’an rundunar dake yaki da garkuwa da mutane suka shiga aiki tukuru inda suka gano wanda yakira mai korafin don ya sanar dashi batan dan uwan nasa.

Hakan yasa aka kama wani mutum mai suna Paul Philips Okiemute,wanda shine yakai rahoton sace Ufom a wurin da yake aiki.

“Okiemute, da yake amsa tambayoyi yace Ufom ne ya shirya yin garkuwa da kansa domin ya karbi kudi a wurin yayansa saboda yayi maganin matsalar kudi da yake fama da ita.

“Tun farko dai babu wanda yayi garkuwa da Ufom, kawai shirine domin ya karbi miliyan 60 kudin fansa a wurin dan uwansa.

“Mutumin da ake zargi yace shine yaboye  namba yakira dan uwan Ufom inda ya bukaci abiya su miliyan 60, daga bisani yan sanda sun kama Ufom Edet Udoh, kuma ya amince da aikata laifin.

” Ya amsa cewa ya shafe kwanaki uku a wani Otal dake Iyana-Ipaja ba tare cin abinci ba, a yinkurin da yake na karbar kudin.” Famous-Cole yace.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s