INEC Ta Dakatar Da Shirin Yiwa Melaye Kiranye 

Hukumar zabe ta kasa INEC, tace  zata bi umarnin da babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar na dakatarwar wucin gadi kan kiranyen da ake shirin yiwa Sanata Dino Melaye. 

Hukumar ta bayyana haka a wata sanarwa da Prince Adedeji Soyebi, yafitar Kwamishinan hukumar  mai kula da harkokin sadarwa da kuma ilimantar da masu kada kuri’a, yafitar jiya Alhamis a Abuja.

Soyebi yace hukumar ta dau wannan mataki ne bayan da ta duba hukuncin kotun na ranar 6 Ga. Yuli, a taron da hukumar ta sabayi a duk mako.

Kotun ta bada umarnin duk mutanen dake da hannu a shirin kiranyen da su dakata har sai lokacin da zata cigaba da sauraran shari’a.

Melaye ya bukaci kotun da ta dakatar da hukumar zabe daukan duk wani mataki akan korafin kiranye da hukumar ta samu da ga mutanen mazabar Kogi ta yamma wacce Melaye,  ke wakilta a majalisar dattawa.

“A matsayin mu na hukuma dake bin doka sau da kafa, INEC zata bi umarnin kotun.

“Amma kuma hukumar ta yanke daukar matakin gaggawa, na ganin an saurari shari’ar da sauri an kuma yanke hukunci.

“Yayin da kotu ta dage sauraran korafin zuwa ranar 29 Ga.Satumba, dokar hukumar zabe ta bata damar kammala aikin yin kiranye cikin kwanaki 90 daga ranar da ta karbi korafin, ” yace.

Kwamishin yakara da cewa hukumar ta ja hankalin  alkalin alkalai na kasa  kan umarnin kotun.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s