AMFANIN ZOGALE GOMA SHA TAKWAS (18) GA JIKIN DAN-ADAM

AMFANIN ZOGALE GOMA SHA

TAKWAS (18) GA JIKIN DAN-ADAM

Ana Bukatar Jama’a su yada wannan
Post zuwaga Sauran Al’umma domin
Qaruwa da Juna.
.
1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a
sha kamar shayi domin maganin Olsa
(ulcer).
.
2- Ana shafa danyen ganyen zogale
akan goshi domin maganin ciwon kai.
.
3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko
wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa
danyen ganyen zogale, Insha – Allah jinin zai tsaya.
.
4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya
hada garin zogale da man zaitun ya shafa.
.
5- Ana sanya garin zogale akan wani
rauni ko gembo domin saurin warkewa.
.
6- Sanya garin zogale a cikin abinci
yana maganin hawan-jini da kuma karama
mutum kuzari.
.
7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa
kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon
shawara.
.
8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga
ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da
ciwon kunne.
.
9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen
zogale da zuma dan karin nono.
.
10-Wanda ke fama da yawan fitsari
wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.
.
11-Idan aka tafasa furen zogale da
albasa aka sha kamar shayi yana maganin
sanyi.
.
12-Haka ma cin danyen zogale yana
maganin tsutsar ciki ga yara.
.
13-Ana daka ganyen zogale da
‘ya’yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.
.
14-Ga mai fama da sanyin kashi ko
wani kumburi zai soya ‘ya’yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.
.
15-A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan
da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro
da kuma kimba domin karin karfin da namiji
da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.
.
16-A daka saiwar zogale da ‘ya’yan
kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).
.
17-Haka kuma idan mutum yana
fama da ciwon Aids zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.
.
18-Haka kuma mai fama da Typhoid da
malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.

 

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s