SHIN KANA YANKAN LEMU KAMAR YADDA YA KAMATA?

*Shin Kana Yanka Lemo Yadda ya Kamata?*

A wata kotu dake Wudil ne wata mata ta kai karar mijinta kotu inda take zarginsa da cewar bai iya yanka lemo ba.

A ranar da aka gabatar da kara a kotu:

*Alkali ga wanda akayi kara*:

Matarka tana zarginka da cewa ba ka iya yanka lemo ba.

*Wanda akayi kara:*

Cikin mamaki yace; Allah ya gafarta Mallam tayaya za’a dubi mutum kamata ace wai ban iya yanka lemo ba, anan ya bukaci da a kawo lemo ya yanka.

Alkali yasa aka kawo lemo da wuka aka bashi, sai ya yanka kuwa.

Alkali ya dubi Matar yace; Malama kince bai iya ba, gashi ya yanka.

Sai Matar tace Allah ya gafarta Mallam akawo min na yanka a gani, za’a san bai iyaba;

Alkali yasa aka bata lemon da wuka.

Da aka bata sai ta kama lugugutawa har sai da yayi ruwa sosai, sa’ilin nan ta sanya wuka ta yanka, ai tana yankawa sai ruwa yana ta zuba.

Sai ta kalli Alkali tace Allah ya gafarta Mallam wanene yafi iyawa?

Alkali yace haka ne, gaskiya mijinki bai iya yanka lemo ba to amma na bashi biko ki je ki koya masa, sai Alkali kuma ya kalli wanda akayi kara, to, kaga yadda ake yanka lemo kuma kayarda cewa kai baka iyaba, saboda haka ka koma gida ka baiwa lemo hakinsa sosai!!!

*Da fatan kaima kana yanka lemo yadda ya kamata*. Ameen!

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s