Brazil ta hana amfani da Whatsapp

Wata kotu a Brazil ta umarci rufe kafar sada zumunta a wayoyin zamani wato Whatsapp a duk fadin kasar.

Wata kotu a kasar Brazil ta yanke hukuncin toshe kafar sada zumunta a wayoyin zamani wato Whatsapp a duk fadin kasar. A cewar kotun ta dauki wannan matakin ne biyo bayan gaza gabatar da cikakkun bayanai a kan wani da ‘yan sanda ke gudanar da bincike a kan shi. Kasar Brazil tana cikin kasashen da ke da yawan masu amfani da kafar sadarwar ta Whatsappa da ke baiwa dinbin matasa da sauran al’umma damar sada zumunta.

Wannan dai ba shi ne karon farko da kanfanin na whatsapp mallakin Facebook, ke cece-kuce da kotunan da ke kasar Brazil a kan rashin ba da bayanai ga jami’an tsaro a kan mutanen da ke amfani da kafar. A yanzu dai kotu ta ce duk kamfanonin waya da ba su dau matakan toshe kafar ta Whatsapp ba za su fuskanci tara na kimanin dalar Amurka 15,265. kamfanin na Whatsapp bai yi martani a kan wannan hukuncin ba tukuna.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s