Wani Limamin Coci Yayi Kira Da A Rage Kudin Aikin Hajjin Bana 

Limamin majami’ar Christ Evangelical Intercessory Fellowship Ministry dake  Sabon Tasha a Kaduna, Pastor Yohanna Buru yayi kira ga gwamnatin tarayya da kuma hukumar Alhazai ta kasa da suka gaggauta rage kudin aikin hajjin bana domin bawa Musulmi damar sauke daya daga cikin shika shikan musulunci.

Fasto Baru yayi wannan kiran ne lokacin da ya kaiwa wani Malamin addinin musulunci dake Barnawa ziyara, inda yace zuwa aikin hajji na daya daga cikin shika shikan musulunci,kuma ya wajaba ga duk musulmin da yake da hali.

Baru yace “Tsadar da kujerar aikin hajji tayi a bana har takai Naira miliyan 1.5 zaisa musulmi da dama baza su samu zuwa kasa mai tsarki ba, saboda haka muna kira ga gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin jihohi da dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar aikin hajji da su lalubo hanyoyin da za a rage kudin domin mutane su samu damar sauke farali.

“Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasa yawan mutane dake zuwa aikin hajji kuma idan Sukaje sunayin addu’ar samun zaman lafiya  da kuma cigaban kasarnan saboda haka muna kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su shiga cikin maganar kafin lokaci ya kure.”

Baru yakara da cewa a matsayinsu na biya addinin Kirista sun damu matuka  kan yarda kujerar aikin hajjin  bana tayi tsada.

Anasa jawabin Mallam Gambo Abdullahi Barnawa ya godewa malamin addinin kan yadda yanuna damuwarsa akan kudin kujerar  aikin hajjin.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s