RAAYI: SAKKWATAWA MU FARKA

RAAYI: SAKKWATAWA MU FARKA

July 04, 2017

Abin da ke faruwa a Sakkwato tsakanin gidan Sarkin Musulmi da zuri’ar Sardauna ya nuna hatsarin rashin Dattawa a cikin al’umma, mussaman ma a Sakkwato inda nan ne zafin yake fitowa.

Mafi rinjayen Dattawan da ake dasu yanzu ga dukkan alamu abin duniya ya fi dauke musu ido, fiye da mutunci da kimar wadanan gidajen biyu dake tsima juna da maganganu marasa amfani.

Amma ache wannan rikicin har ya kai kusan watanni fiye da goma, an kasa warware shi anan Sakkwato, har ya fita waje, amma ga na Kano cikin dankankanin lokaci anyi magana; wasu sun dauka abin ya zama tarihi.

Daraja da kwarjini sarauta Sarkin Musulmi tafi karfin mutum daya komi girmansa ko ikonsa, haka ma mutunci da girma na Sardaunan Sakkwato yafi karfin wani mutum shi kadai ya wargaza shi ko bata masa suna.

Kodai ayi gyara, ko mu ci gaba da zama abin dariya a fili da zuci, muna ganin ana mutunta Sakkwato amma a zuci ana yi mana kallon marasa sanin kimar kansu.

Idan da akwai Dattawa masu dattakon ganin an warware matsalar ba don neman dan abin masarufi ba, dattawa wadanda suke da daraja da kima da ba ruwansu da kwadayin abin hannun kowa; dole ache anyi maganin wannan matsalar tun ma bata kai matsayin ta a yanzu ba.

Su kansu matasan da ake amfani dasu wajen iza zafin kiyyaya a kafofin sadarwa, ba su san tarihi da minene daraja ga tarihin baya ba,  illa damuwa da dan abin cefane da suke karba don biyan bukatar wasu.

Sarkin Musulmi ya dace ya kalli wannan matsalar da idon basira, don kuwa har wasu daga waje sun shigo suna iza wutar kiyyaya akan wannan lamarin, ganin sakacin da aka nuna ga aiwatar da sulhu na gaskiya a tashin farko ga warware matsalar nan.

Baya ga hakan ma akwai wasu muhimman mutanen da suka shigo da wasu yan rubuce rubuce da zasu yiwa tarihi da zamantakewa ta Daular Usumaniyya illa.

Magajin Garin Sokoto ya bar kalaman haka nan, ya dace ya lura da ababen dake faruwa a cikin kalamansa, da makomar tarihi akansu, suna da hatsari ga wargaza daraja da mutuncin wannan sarauta a gaba; abin da ba zai yiwa kowa dadi ba har ma da shi kansa.

Ita kanta gwamnatin jahar Sokoto tafi kowa laifi, don tayi sakaci ko daukar bangare a rikici, abin da ya nuna bata hobbasa ba duk da yake tana da wuka da nama dangane da tun farko rashin daukar mataki mai zafi mussaman ma a kashe wannan wutar a koyaushe taso.

Idan har gwamna Tambuwal wanda yake shine Matawwalen Sakkwato, Basarake dake da daraja da kima ga masarautar da take fuskantar hatsarin zubewar daraja da kima yana da ra’ayi, dole ne ya kalli rikicin a fuskar cikin gida, yayi amfani da ikonsa na tsarin mulki ya hana yaduwarsa, dole ne ya nuna ma duniya bukatar ganin kai karshen wannan matsalar.

Ya nuna shine gwamna jahar Sokoto wajen hana yada wadanan batutuwa dake da rashin amfani da kuma cutar da daraja sarauta da kimar Daular Usumaniyya.

Tarihi ba zai taba yafe mana ba, idan muka yi shiru ana wargaza daraja da kimar abin da muka ginu akansa na addini, mutunci da tarbiyya da iyaye da kakkani suka bayar da rayuwarsu da lokacin su akai.

Sakkwatawa mu farka

Dingyadi, ya rubuta daga Sokoto.

1 thought on “RAAYI: SAKKWATAWA MU FARKA

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s