Kotun Tarayya Dake Kaduna Ta Kori Karar Da El-Zakzaky Ya Shigar A Gabanta

 

 

Babban kotun tarayya dake zamanta a Kaduna ta kori kara tsakanin shugabannin kungiyar yan uwa musulmi da akafi sani da Shi’a wato Ibrahim elzakzaky,matarsa Zeenat da kuma rundunar sojin Najeriya tare da wasu mutane uku kan abinda kotun ta kira  rashin bin ka’idojin kotu.

Mai karar wanda shine shugaban kungiyar Shi’a a Najeriya , sheikh Ibrahim El-zakzaky, yakai karar  rundunar sojin Najeriya ,Babban hafsan sojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai,  ministan shariar Najeriya da kuma gwamnatin jihar Kaduna,gaban babbar kotun tarayya dake Kaduna.

An tuhume su da laifin kashe yayan Zakzaky biyu, da kuma lalata masa gida a rikicin da yafaru tsakanin mabiya  yan kungiyar ta shi’a da kuma sojoji a cikin watan Disambar 2015.

Idan za’a iya tunawa wata kotun tarayya dake Abuja karkashin mai Shari’a Gabriel Kolawole, tun farko ta yanke hukunci kan yadda aka tauye masa hakkinsa ta hanyar tsare shi tare da maidakinsa   ba tare da ka’ida ba,ya kuma bada umarnin a sake su  cikin kwanaki 45  sannan a samar musu da muhalli mai kyau kana a biyasu diyar miliyan 50.

Da yake yanke hukuncin da ya dauki tsawon mintuna 45 alkalin kotun Salah Musa Shuaibu, yayi nuni da cewa idan aka ci mutuncin kotu to ya zama dole a kori kara.

Ya shawarci Lauyoyi kan su daina shigar da Shari’a daya a gaban kotuna daban daban.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s