An Yankewa Shugaban Makarantar Sakandire Daurin Rai Da Rai Kan Laifin Yiwa Yarinya Yar Shekara 12 Fyade

Babbar  kotun Ado-Ekiti  dake jihar Ekiti,ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan Taiwo Ajayi, shugaban wata makarantar sakandire bayan da ta same shi da laifin yiwa yarinya yar shekara 12 fyade. 

An rawaito cewa Ajayi ya yaudari yarinyar zuwa ofishinsa inda yayi lalata da ita akan teburinsa bayan da ya toshe mata baki da hankici.

Alkalin kotun Oluwatoyin Abodunde, wanda ya zartar da hukuncin ,yace kotu ta samu shugaban makarantar  da aikata  laifi kamar yadda ake zarginsa.

Abodunde yaki amincewa da rokon mai laifin,kan a tausaya masa saboda wannan ne laifinsa na farko, yana da yaya sannan kuma yana da tsohuwar uwa da yake daukar dawainiyarta.

” Masu gabatar da kara sun gabatarwa da kotu kwararan hujjoji dake nuni da cewa lallai mai laifin ya aikata abinda ake zarginsa,” yace.

” Laifin yiwa kananan yara fyade kullum karuwa yake a gari  cikin yan kwanakin nan, a ganina hukuncin da masu yin dokoki suka samar an samar dashi ne domin a tsorata mutane kan su guji aikata laifi da kuma kare yara kana da daukaka darajarsu.

“Lauya mai kariya yana rokon kotu da ta sassauta hukunci zuwa biyan tara kadai,mai makon horo.Amma  tambayata anan itace:wa zai biya yarinyar  tabon da akayi mata na  damuwar da zata shiga har tsawon rauywarta da kuma na azabar dake tattare da yin fyade.?

” Bazan iya kaucewa hukunci da doka ta tanadar  ba,a wannan gabar,mutumin da ake kara an same shi da laifi kamar yadda ake zargi saboda haka na yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.”

An dakatar da Taiwo daga aiki a ranar 18 Ga Maris, 2014 domin ya fuskanci hukunci kan abin da ya aikata.

Lokacin da mutumin ya aikata laifin yana matsayin Mataimakin Shugaban makarantar yan mata ta S.t Marry ,dake Ikole Ekiti.

Malamai biyu ne dai suka je ofishin shugaban makarantar amma basu samu damar shiga ba har sai bayan mintuna 30 inda suka kamashi da aikata laifin.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s