Zauren Fiqhu: Maganin Hawan Jini Da Ulcer

Kasancewar jama’a da dama suna fama da wadannan matsalolin shi yasa muka zakulo muku wata fa’ida mai saukin hadawa domin ajarraba.

Allah yasa adace:

ASAMU :

1. Garin Habbatus Sauda Cokali 7.

2. Garin tafarnuwa cokali 5.

Ahadasu acikin zuma kofi guda, agauraya a ajiye. Sannan marar lafiyan zai rika shan cokali 3 kullum da safe bayan ya karya. (after breakfast).

Zai ci gaba da yin haka har kwana 20, sanan bayan nan asamu Man Habbatus Sauda irin na Misra ko Pakistan ko Saudia, kullum arika zuba cokali guda acikin ruwan shayi ana sha tare da zuma ko sikari Safe da yamma.

Wannan maganin zai yi amfani sosai ga Masu fama da chutar Ulcer (Olsa) ko Rashin fitowar fitsari ko rikicin jinin haila. Ko matar da ruwan nononta ba ya zuwa sosai. Ko kuma masu fama da matsalar Pneumonia ko Asthma.

Kuma ana so mutum ya kiyaye aikata duk Abubuwan da zasu iya motsa masa rashin lafiyarsa ayayin da yake shan maganin nan.

Insha Allah za’a ga abin mamaki wajen samun waraka daga Allah (SWT) domin kuwa tushen wadannan magungunan yana nan acikin Alqur’ani da Sunnar Manzon Allah (saww).

Idan an jarraba an dace, tukwicinmu shine ayi ma Annabi (saww) salati kuma ayi ma Kasar nan addu’a Allah ya bamu zaman lafiya, Allah ya kawo ma al’ummah sassaucin halin da suke ciki. Ameeen.

1 thought on “Zauren Fiqhu: Maganin Hawan Jini Da Ulcer

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s