Iyalina Sun Zuba Jari A Harkar Gidaje A Dubai Tun Kafin Na Zama Babban Hafsan Soja – Buratai

 

Babban hafsan Sojojin Kasa na Najeriya, Tukur Yusuf Buratai,  yace iyalinsa sun zuba jari a Dubai dake Kasa Hadaddiyar Daular Larabawa tun kafin yasan zai zama babban hafsan sojin Kasan Najeriya. 

Buratai ya fadi haka a tattaunawar da yayi a shirin Hard Talk na gidan Talabijn na BBC  a ranar Talata, yace,iyalinsa suna gudanar da kasauwanci  na kashin kansu,kuma suna da karfin  da zasu mallaki gida a Dubai.

” Wani bangare na kadara kamar zuba jarine, Iyalina suna kasuwancinsu daban, yakamata ace suna da kudin da zasu iya mallakar gida a Dubai,”Buratai yace.

” Irin gidan da muke magana akai bashi mu mutane suke nufi ba.

” Gidan dana zuba jari a ciki a shekarar 2013 tun kafin nasan zan zama shugaban sojoji, amma mutane suna zargina kamar yau na aikata haka. ”

Da yake magana kan musayar yan matan Chibok da akayi da wasu kwamandodin Boko Haram, yace an cimma matsayar yin haka ne domin bukatar kasa baki daya.

Yace wannan ba hukuncin sojoji bane, yan siyasa ne suka dauki matakin yin haka.

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s