Dangote Ya Musalta Zargin Da Ake Masa Na Bawa Tsohon  Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Cin Hancin Naira Miliyan 100

 

Mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afirika, Alhaji Aliko Dangote ya musalta zargin da ake masa na bawa tsohon  shugaban majalisar dokokin jihar Kano kudi naira miliyan 100 domin su dakatar da binciken da sukeyi akan sarkin Kano Muhammad sunusi II. 

Dangote yace kwamitin binciken da majalisar dokokin jihar ta kafa kada ma yabata lokacinsa.

“Ga baki dayan maganar karyace, “mai magana da yawun rukunin kamfanonin Dangote Tony Chiejina yace.

Yace Zargin bashi da tushe bare makama karyace tsagwaronta .

Jaridar Daily Nigerian ce ta rawaito cewa Dangote ya bawa shugaban majalisar naira miliyan 100 domin su dakatar da binciken.

A lokacin da yake mai da martani kan zargin da ake masa a  wata zantawa da manema labarai ranar 20 ga watan Yuni,Rurum ya bayyana labarin a matsayin karya da aka tsara domin a bata masa suna da kuma a saka baki dayan majalisar cikin rudani.

Inda yabawa jaridar ta Daily Nigerian wa’adin mako guda kan ta janye labarin ko kuma ta fuskanci matakin Shari’a.

Rurum yace bai taba ganawa da Dangote ba ballantana suyi maganar karbar cin hanci.

Yace saka bakin da mukaddashin shugaban Kasa Yemi Osinbajo, yayi da kuma sauran yan Najeriya shine yasa suka dakatar da binciken.

Mista Chiejina ya fadawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a daren Litinin  cewa, zargin yana batawa Dangote suna a idon jama’a.

“Aliko Dangote  bai san Kabiru Alhasan Rurum ba, ballantana ya zama abokinsa kamar yadda rahoton jaridar yanuna. “Chijiena yace.

A ranar Litinin ne dai Rurum yayi murabus daga kujerarsa ta shugaban kan zargin karbar cin hanci da ake masa.

 

Source: Arewa24 News

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s