Ta’aziyar Dan Masani: MUHAMMADU BUHARI YA AIKAWA GWAMNAN KANO WATA WASIKA MAI BAN TAUSAYI

Ta’aziyar DAN MASANI:
MUHAMMADU BUHARI YA AIKAWA GWAMNAN KANO WATA WASIKA MAI BAN TAUSAYI

Shugaba Muhammadu Buhari ya aiko TAKARDA inda yake takaicin rashin Maitama Yusuf – An yi babban rashi a Najeriya gaba daya Inji Shugaban kasa Buhari – Tsohon Ministan Kasar ya rasu ne Jiya a Asibiti da ke kasar Masar Shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta wasika ga Gwamnan Kano Dr. Ganduje.

Shugaban Kasar yana ta’aziyya ne ga Jama’ar Kano duka game da rashin Dan Masani. Dan Masanin Kano mutum ne mai baiwar magana har bayan ya makance Inji Buhari. Hoton Dan Masanin Kano tare da Buhari daga Jaridar NigerianMonitor Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikowa Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje wasikar ta’aziyar tsohon Ministan Najeriya kuma Dattijon Arewa Yusuf Maitama Sule.

Shugaba Buhari yace an yi babban rashi a Najeriya.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa ba za a taba mantawa da Dan Masani ba.
Shugaba Buhari yace Marigayi Dan Masanin Kano ya taimakawa Shugabannin Najeriya na farko a lokacin yana Minista. Har ya bar Duniya ba a taba samun sa da wani rashin gaskiya ba. Shugaba Buhari yace har ya bar Duniya yana koyon darasi wajen Dan Masanin Kano idan su ka zauna.

A jiya ne shi ma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya taya sauran Jama’a ta’aziyar Marigayi Ambasada Yusuf Maitama Sule da ya cika. Gwamnan yace an yi babban rashi a Najeriya.

Source: Naij.com

2 thoughts on “Ta’aziyar Dan Masani: MUHAMMADU BUHARI YA AIKAWA GWAMNAN KANO WATA WASIKA MAI BAN TAUSAYI

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s