IFTILA’I A KARAMAR HUKUMAR ILLELA.

Alhakika Allah na jarabtar Bayinsa ta kowace irin hanya. A Karamar Hukumar Mulkin Illela, musamman a Garin Illela, Amarawa, Araba, Bakin Dutsi, Sonani da sauran Garuruwa da dama, sun samu kansu cikin RUDANI, a sanadiyar Ruwan Sama da Iska mai tsananin karfi da yayi sanadiyar:

= Rushewar Gidajen Kwana akallah Dari da Goma sha Hudu + (114+).

= Lalacewar Gidajen Kwanan Al’umma akallah Dari Biyu da Ishirin da Ukku+ (223+).

= Lalacewar Makarantun Gwamnati da masu zaman Kansu.

= Hasarar Rayukka da Kwantar da wasu a Gadon Assibi.

= Hasarar Dukiya mai tarin yawa.

= Mutuwar Dabbobi da dama.

Abin tausayi shine, kashi Tamanin da Tara (89,%) na Mutanen da sukayi Hasarar Matsugunni, Talakawa ne, wadanda basu da karfin mallakar Abincin gobe, ballanta samun Muhallin zama cikin dankankanen lokaci.

Bayan bukatar da ke akwai na neman taimakon Gwamnati, akwai bukatar Al’umma su taimaka ma wadannan Mutane.

Lokaci kadan bayan faruwar wannan Ibtila’i, Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Illela (Hon. Abdullahi Haruna Illela), Shugaban Jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Mulkin Illela (Alh. muhammadu Musa Sarkin Alaru), Sakataren Karamar Hukumar Mulkin Illela (Alh. Murtala Sabo Yabo), Shugaban Ma’aikata – DPM ( Alh. Nasiru Umar Alkali), Director Ayukka da Gidaje ( Engr. Umar Mai Wurno Hammah Ali), Galadiman Illela (Engr. Aminu A. Musa Illela). Kwamitin Gwamnatin Jiha, Jami’an SSS, NSCDC (Civil Defence) da sauran Ma’aikata, sun hanzarta kai ZIYARAR JAJANTAWA tare da wakiltar Gwamnati akan gani da kiyasin hasarar da ta afku.

19554216_10209232784523354_504038177145484103_n19553875_10209232799763735_2806003330489034827_n19554315_10209232789803486_7835869509694146126_n19642426_10209232796843662_4307051736735303142_n

A sa’ilin wannan zagaye, Kwamitin karkashin Jagoranchin Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Illela da Kwamiti mai wakiltar Gwamnatin Jiha tare da ayarin “Yan Jarida daban daban sun samu ziyartar Gidaje da dama.

Allah ya tausayawa wadannan Al’umma baki daya ya kuma kara tsarewa.19554335_10209232784883363_4367651989505795002_n19601104_10209232783843337_1797515859838528641_n

3 thoughts on “IFTILA’I A KARAMAR HUKUMAR ILLELA.

 1. Allah ya daukaki wannan karamar hukuma da kuma shuwagabannin ta masu son ci gaban al’ummar wannan karamar hukuma. Tare da fatan wannan shafin zai taimaka wajen kawo chanji mai ma’ana a wannan karamar hukuma, Jaha, da kasa baki daya.
  Alal haqiqa akwai abubuwa masu yawa dake cima al’ummar wannan yanki namu tuwo a kwarya, musamman abinda ya shafi wutar lantarki da kuma ko inkula da gwamnatocin da suka gabata da kuma wadanda ke mulki a yanzu suke nunawa ga wannan garin mai dinbin tarihi da kuma taka muhimmiyar rawa ta fannin kasuwanci da siyasa. Amma a wajen rabon mukaman gwamnati an mayarda wannan yanki saniyar ware.
  lalle lokaci yayi da ya kamata al’ummarmu su farga.

  Like

 2. Batun wutar lantarki da cigaban gari kuma wannan sai a wajen Allah za’ayi hisabi, don al’amari Wanda ya shafi wutar lantarki anan karamar hukumar Illela mukan shafe wata uku zuwa hudu babu ko alamar wuta alhali akwai wutar, amma sai a chanza akalarta zuwa wani waje.
  Mu talakawan wannan yanki muna kira da kakkausar murya ga wadanda abin ya shafa (shuwaganni) su farga don nemo muna hakkinmu.

  Like

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s